Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada al'adun muslunci cewa, an fara gudanar da baje kolin kayan fasahar rubutun ayoyin kur'ani na wasu daga cikin marubuta Iraniyawa a kasar Girka.
Daga cikin fitattun masu fasahar rubutun da suka halarci har da Mujtaba Sabzeh da kuma Fatima Kikawusi, wadanda dukkanin fitattun masu fasahar rubutun ayoyin kur'ani a kasar Iran.
Wannan baje koli da aka fara gudanar a jiya Laraba, zai ci gaba har zuwa wasu kwanaki a nan gaba, inda mutane suke ci gaba da halartar wurin domin duba irin wannan fasaha ta rubutun ayoyin kur'ani da salo daban-daban.