IQNA

22:45 - May 02, 2018
Lambar Labari: 3482624
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman taro na kasa da kasa kan bunkasa harkokin tattalin arziki na kasashen musulmi a Masar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shafin yada labarai na al'ikhbariyya na kasar Masar ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da zaman taron ne tare da halartar masana harkokin tattalin arziki daga kasashen duniya.

Dr. Saifi shugaban jami'ar kasuwanci ta birnin Iskandariyya ya gabatar da jawabi a wurin taron, inda ya bayyana cewa akwai abubuwa da dama da ya kamata a amfana da su ta fuskar tsarin tattalin arziki da musulunci ya zo da shi.

Haka nan kuma ya jaddada wajabcin kara karfafa ayyukan bankunan muslucni a  cikin kasashen musulmi domin su samu zama a kan kafafunsu.

Babbar manufar gudanar da taron dai ita ce tattajnawa kan yadda za a fitar da sabbin hanyoyi da za su taimaka ma tattalin arzikin musulmi, da hakan ya hada da karfafa bankunan muslunci da kuma samar da hanyoyin bayar da horo kan harkokin tattalin arziki da saka hannayen jari da kasuwanci, domin yaki da talauci da ya addabi da dama daga cikin kasashen musulmi.

3711112

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، hanyoyi ، kamfanin dillancin labaran iqna ، yaki ، talauci ، IQNA ، tattalin arziki ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: