Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar talabijin ta Russia Today ta bayar da rahoton cewa, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov a wani taron manema labarai da ya gudanar yau tare da takwaransa na kasar Jordan Aiman Safadi da ke ziyara a Moscow, ya bayyana matukar damuwarsa dangane da halin da ake ciki a Palastinu, da kuma irin matakan da Isra’ila take dauka a Quds.
Lavrov ya ce birnin Quds na dukkanin mabiya addinai da aka saukar daga sama ne, da hakan ya hada yahudawa da kiristoci da kuma muuslmi.
Kalaman na ministan harkokin wajen Rasha na a matsayin martani ne ga matsayar da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka ne na ayyana birnin Quds a matsayin babban birnin haramtacciyar gwamnatin yahudawan Isra’ila.