IQNA

23:49 - May 06, 2018
Lambar Labari: 3482636
Bangaren kasa da kasa, masarautar mulkin kama karya ta Bharain ta hana shigar da littafan mazhabar shi'a ga wadanda ake tsare da su a gidajen kason kasar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Rim Sha'alan wata mai kare hakkokin 'yan adam ta bayyana cewa, masarautar mulkin kama karya ta Bharain ta hana shigar da littafan mazhabar shi'a ga wadanda ake tsare da su a gidajen kaso

Ta ce ta bi diddigin wannan lmarin, inda ta gane cewa daga cikin littafan da aka hana har da littafan addu'oi wadanda ake amfani da su musammana  lokutan bauta a cikin wadannan watanni masu alfarma.

Ta ce ba ta san inda wannan ya zama ya daba wa wata kaida ko dokar kasar ba, musamman ganin cewa dama fursunonin siyasa da ake tsare da akasar mafi yawansu mabiya mazhabar shi'a ne, kamar yadda kuma dama fiye da kasha tamanin cikin dari na mutanen kasar ta Bahrain mabiya mazhabar shi'a ne.

3711678

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamar ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: