IQNA

23:47 - May 08, 2018
Lambar Labari: 3482641
Bangaren kasa da kasa, hauzar Imam Sadeq (AS) da ke garin Komasi na kasar Ghana ta yaye wasu daga cikin dalibanta.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jami'ar musulunci ta Ghana cewa, a yau an gudanar da bikin yaye wasu daga cikin daliban tare da halartar malamai da suka hada da babban limamin birnin.

Daliban sun karbi shedar kamala karatu a matsayin diploma ne a bangaren karatun addini, kamar yadda kuma za su iya ci gaba da karatunsu da wannan shahadar ga mai bukata.

Wannan dai shi ne karon farko da aka fitar da dalibai da suka kamala karatu a na diploma.

An bude wannan makaranta ta Hauza ne a shekarar da ta gabata tare da taimakon jami'ar Almostafa (SAW).

3712482

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، sadarwa ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: