IQNA

Wakilin Iran A Gasar Kur'ani Ta Kasar Malaysia

23:46 - May 10, 2018
Lambar Labari: 3482644
Bangaren kasa da kasa, Mukhtar Dehqan wakilin Iran a gasar kur'ani ta duniya ya kai matakin kusa da na karshe a wannan gasa.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoto daga wurin gasar kur'ani ta Malaysia cewa, Mukhtar Dehqan yana taka gagarumar rawa a wajen wanann gasa, inda ya karanta ayoyi na 59 da 66 a surat Nisa.

Sayyid Jawad sadat Fatemi da ke jagorantar tawagar Iran a gasar ya bayyana cewa, sun gamsu da yadda Dehqan yake gudanar da karatunsa.

Haka nan kuma Muhammad ali Sabeghi shugaban karamin ofishin jakadancin Iran a Malaysia ya bayyana gamsuwarsa matuka kan yadda wannan makaranci yake gudanar da karatu, ta yadda hatta alkalan wurin sun nuna gamsuwa da yadda karatunsa ke gudana.

3713184

 

 

captcha