IQNA

23:49 - May 10, 2018
Lambar Labari: 3482645
Bangaren kasa da kasa, Ana ci gaba da gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta duniya karo na sattin da ake gudanarwa a kasar Malaysia.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau aka shiga rana ta hudu a gasar kur'ani ta duniya da ake gudanarwa a kasar Malaysia, tare da halartar makaranta da mahardata daga kasashen duniya.

Wannan gasa dai ita ce mafi girma da ake gudanarwa a duniya, kamar yadda kuma ita ce mafi jimawa a tarihi, inda  a bana aka cika shekaru sattin ana gudanar da wannan gasa a kasar ta Malaysia.

A ranar Asabar mai zuwa za a gudanar da taron karshe na wannan gasa, tare da halartar manyan jami'an kasar da kuma sarkin kasar ta Malaysia Muhammad na biyar, inda za a bayar da kyautuka na bai daya ga dukkanin mahalarta gasar, kamar yadda za a bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazo a gasar.

3713026

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: