IQNA

Jagora: Dole Ne Kasashen Asia Su Kara Fadada Huldodi A Tsakaninsu

22:50 - May 13, 2018
Lambar Labari: 3482653
Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Sri Lanka Maithripala Sirisena tare da rakiyar shugaba Rauhani ya gana da jagoran juyin juya halin muslunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei.

 

Kamfanin dillancin labaran ina ya habarta cewa ya nakalto daga shafin jagora cewa, a lokacin da yake ganawa da shugaban Sri Lanka a yau, jagoran juyin  juya halin muslunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa, ya zama kan kasashen Asia su kara karfafa alakokinsu da junansu, matukar dai suna son su zama masu ‘yanci a cikin harkokinsu.

Ya ce kasashen Iran da Sri Lanka kasashen masu dogon tarihi, kuma har yanzu alaka tsakanin al’ummomin biyu tana nan kamar yadda take, kuma kasashe ne biyu da suke da kyakkyawar alaka ta kasuwanci da ilimi da al’adu.

Haka nan kuma ya yi kira ga dukkanin gwamnatocin biyu da su aiwatar da dukkanin yarjejeniyoyin da suka rattaba hannu akansu a yau, domin amfanin al’ummomin kasashen biyu.

Shi ma a nasa bangaren shugaban Sri Lanka yay aba da irin ci gaban da alaka tsakanin kasarsa da Iran ke samu, inda ya bayyana Iran a matsayin kasar da tafi mafi yawan kasashen Asia ci gaba ta fuskar ilimi da kimiyya da kere-kere.

3714107

 

 

captcha