IQNA

23:10 - May 21, 2018
Lambar Labari: 3482681
Bangaren kasa da kasa, wasu ‘yan bindiga biyu sun harbe Maulana Habibillah Mingal daya daga cikin jagororin kungiyar jama’at Ulama Islam a Pakistan.

 

Kamfanin dillancin labara iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin almuslim cewa, a jiya wasu ‘yan bindiga biyu sun harbe daya daga cikin jagororin kungiyar manyan malaman musulunci ta jama’at Ulama Islam a Pakistan Maulana Habibillah Mingal,a  lokacin da ya fito daga masallaci za tafi gida.

Bayan faruwar lamarin dai jami’an tsaro sun yi yankin da abin ya faru kawanya.

Har yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kadamar wannan hari.

3716518

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، tafi gina ، malaman muslunci ، pakistan ، Maulana Habibillah Mingal ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: