IQNA

23:29 - May 22, 2018
Lambar Labari: 3482682
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da zama mai taken nazari kan mahangar Imam Khomeni (QS) a kan falsafa da kuma Irfani a kasar Spain.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga bangaen hulda da jama’a na cibiyar yada al’adun musulunci cewa, a jiya an gudanar da zama mai taken nazari kan mahangar Imam Khomeni (QS) a kan falsafa da kuma Irfani a birnin Madrid.

Daga cikin wadanda suka gabatar da jawabai a wurin taron akwa Hojjatol Islam Sayyid Ali Mosawi, sai kuma Raul Gonzales Borens wani masanin falsafa dan kasar ta Spain, sai kuma Sheikh Ibrahim Amal.

Babbar manufar taron dai ita ce yin nazari kan mahangar ilimin falsafa da Irfani a rubuce-rubucen da Imam Khomeni ya yi a wannan bangaren, inda ya wallafa littafai da dama.

3716798

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: