IQNA

23:50 - May 24, 2018
Lambar Labari: 3482691
Bangaren siyasa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasemi ya bayyana furucin miminstan harkokin wajen Moroco da cewa ya yi kama da almara.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasemi ya bayyana furucin miminstan harkokin wajen Moroco da cewa ya yi kama da almara maras kan gado.

A jiya ne ministan harkokin wajen Morocco ya sake maimaita tuhumar da yi kan Iran a kwanakin baya, kan cewa sun yanke alaka da Iran bisa zargin tana taimaka ma kungiyar yan awaren polisario, amma ba tare da ya iya gabatar da wani dalili da zai iya tabbatar da hakan ba.

Qasemi ya ce ministan na Morocco ya fi kowa sanin cewa abin yake fada karya ne, kuma yana yin hakan ne domin dada ma wasu saboda matsaloli tattalin arzikin da kasarsa ke fuskanta, kuma ta hanyar hakan ne kawai kasarsa za ta iya samun abin da take so daga masu juya akalarta.

3717327

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: