IQNA

23:42 - May 27, 2018
Lambar Labari: 3482697
Bangaren kasa da kasa, mutane 100 ne suka kai ga mataki na karshe a gasar kur’ani ta duniya da ae gudanarwa a kasar Qatar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya zwa yanzu ana ci gaba da gudanar da gasar kur’ani a cibiyar Ketara da ke Qatar.

Mutane 1429 ne suke halartar gasar daga kasashe 55 , yayin da mutane 100 ne suka kai ga mataki na karshe, inda daga ckinsu ne za a fitar da wadanda za su zo mataki na daya da na biyu da na uku a dukkanin bangarorin gasar.

Wannan dais hi ne karo na biyu da ake gudanar da wannan gasa, wadda aka fara tun a watan Ramadan na shekarar da ta gabata.

Gasar dai ta samu karbuwa daga sassa daban-daba na duniya, ganin irin tsarin da aka yi wajen gudanar da ita yana da burgew.

A shekarar da ta gabata wadanda suka lashe gasar sun fito ne daga kasashen Libya, Masar, Morocco da kuma Aljeria.

3717940

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Masar ، Qatar ، Libya ، gasar kur’ani ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: