IQNA

23:02 - May 28, 2018
Lambar Labari: 3482700
Bangaren kasa da kasa, an kammala gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasashen gabashin Afirka a birnin Darussalam na Tanzania.

 

Kamfanin dillancin labara iqna ya habarta cewa, shafin yda labarai na arab yaum ya bayar da rahoton cewa, a jiya ne aka kammala gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasashen gabashin Afirka a birnin Darussalam tare da halartar manyan baki.

Daga cikin bakin da suka samu halartad taron rufe gasar dai har da firayi ministan kaar ta Tanzania Kasim Majaliwa, da kuma wasu daga manyan malaman kasar.

Shekaru 19 kenan ana gudanar da wannan gasa a kasar Tanzania, wadda take samun halartar makaranta da mahardata daga sassa na kasar, da kuma wasu daga cikin kasashen nahiyar Afirka.

Sheikh Abdulkadir Bin Muhammad Ahdal shugaban cibiyar addinin muslunci ta Hikma ta kasar Tanzania, a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wurin taron ya bayyana cewa, gasar kur’ani tana da babban tasiri wajen yada koyarwar kur’ani da kuma karfafa zukatan matasa musulmi kan sha’anin kur’ani.

Kasashen da suka halarci gasar dai sun hada da Tanzania, Keya, Jibouti, Uganda, Rwanda, Burundi, Ghana, Somalia, Najeriya, Afirka ta kudu, Sudan, Muzambik, Congo, Ethiopia, Aljeriya, Komoros da Nijar.

Tanzania dai na a gabashin nahiyar Afirka, fiye da kashi 40 na mutanen kasar musulmi ne.

3718251

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: