IQNA

23:05 - May 28, 2018
Lambar Labari: 3482701
Bangaren kasa da kasa, babbar majami’ar birnin Arlinton na jahar Virginia a kasar Amurka ta bude kofofinta ga musulmi a cikin watan Ramadan.

 

Kamfanin dillancin labaran alhurra.com ya bayar da rahoton cewa, tun daga lokacin da watan Ramadan ya kama, majami’ar kiristoci ta Arlinto take gayyatar musulmi domin su yi buda baki.

A jiya majami’ar ta gayyaci sauran mabiya addinai da suka hada da kiristoci da yahudawa domin su zo su taya musulmi murnar shan ruwa, inda suka ci abincin buda baki tare da musulmi.

Wannan majami’ar tana daga cikin wasu majami’oin Amurka da suke kare hakkokin musulmi, tare da nuna wa Amurkawa cewa musulmi mutane ne masu son zaman lafiya, tare da kore duk wani zargi na ta’addanci a kan addinin musulunci da musulmi.

3718115

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Amurka ، virginia ، kofoffinta ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: