Kamfanin dillancin labaran alhurra.com ya bayar da rahoton cewa, tun daga lokacin da watan Ramadan ya kama, majami’ar kiristoci ta Arlinto take gayyatar musulmi domin su yi buda baki.
A jiya majami’ar ta gayyaci sauran mabiya addinai da suka hada da kiristoci da yahudawa domin su zo su taya musulmi murnar shan ruwa, inda suka ci abincin buda baki tare da musulmi.
Wannan majami’ar tana daga cikin wasu majami’oin Amurka da suke kare hakkokin musulmi, tare da nuna wa Amurkawa cewa musulmi mutane ne masu son zaman lafiya, tare da kore duk wani zargi na ta’addanci a kan addinin musulunci da musulmi.