Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin Almanar cewa, a ranar Juma’a mai zuwa kungiyar Hizbullah ta kasar Lbanon za ta gudanar da tarukan ranar Quds a yankin Marun Ra’as da ke kan iyaka da Palastinu.
Sayyid Hassan Nasrullah babban sakataren kungiyar Hizbullah zai halarci wannan taro.
A kowace ranar Juma’a ta karshen kowane watan Ramadan ana gudanar da tarukan ranar quds a wannan yankin, amma a shekarar bana taron dauki sabon salo.