Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tun a daren jiya ne aka fara gudanar da tarukan raya dararen lalatul qadr a birnin Adelaide na kasar Australia.
A taron na jiya an gudanar da salloli da kuma jawabai kan sarar da aka a yi ya wa Imam Amirul muminin Ali (AS) wanda hakan ya yi sanadiyyar shahadarsa.
Baya ga ahka kuma an gabatar jawabai kan shahadarsa, daga cikin masu jawabi akwai Gholam Ali Haidari, sai kuma Idris Hassan, wanda ya karanta addu’ar Jaushen kabir da sauran addu’oi na wannan dare mai albarka.