Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, mutanen wani kauye a kasa Uganda sun karbi addinin muslunci baki dayansu a hannun wasu masu wa’azi ‘yan kasar Oman.
Bayanin ya ce dukkanin mutanen kauyen ne suka musulunta bayan an yi musu wa’azi, inda suka bar addinin kiristanci suka koma musulunci.
Kasar ganda tana a gabashin nahiya Afirka ne, kuma akasarin mutanen kasa kiristoci ne, kimanin kashi 12 kuma musulmi ne.