IQNA

Harin Ta’addancin Isra’ila Palastinawa Masu Jerin Gwano

23:32 - June 09, 2018
Lambar Labari: 3482742
Harin Ta’addancin Isra’ila Palastinawa Masu Jerin Gwano
Bangaren kasa da kasa, Harin wuce gona da iri da sojojin gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan al'ummar Palasdinu da ke gudanar da zanga-zangar ranar Qudus ta duniya a jiya Juma'a a yankin Zirin Gaza, akalla Palasdinawa 4 ne suka yi shahada.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna, ma'aikatar lafiya a yankin Zirin Gaza ta fitar da sanarwar cewa: Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun bude wutan bindiga kan al'ummar Palasdinu da suke fito zanga-zangar ranar Qudus ta duniya a jiya Juma'a a yankin Zirin Gaza, inda suka janyo shahadar Palasdinawa akalla 4 tare da jikkata wasu fiye da 500 na daban.

Tun bayan kammala sallar Juma'a a Masallacin birnin Qudus a jiya Juma'a al'ummar Palasdinu suka fara gudanar da zanga-zangar ranar Qudus ta duniya a yankuna daban daban na Palasdinu.

Kamar yadda a jiya Juma'a ce dai aka gudanar da Ranar Qudus ta Duniya a sassa daban daban na duniya, inda ake gudanar da zanga-zangar lumana da taron gangami domin jaddada goyon baya ga al'ummar Palasdinu da ake zalunta da Masallacin Aqsa da ke fuskantar babbar barazana daga Yahudawan Sahayoniyya 'yan mamaya.

3721041

 

 

 

 

 

captcha