Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar fox cewa, an rufe wata tashar talabijin mai alaka da kasar Saudiyya a garin urtaba na Spain ba tare da bayyana dalilin yin hakan ba.
Wannan tasha dai tana karkashin wani mutum ne mai suna Fauzan wanda kuma yana dauke ne da akidar wahabiyanci, amma a cikin ‘yan watannin da suka gabata tashar bata biyan albashi kan kari ga maia’ikatanta.
Bayan haka kuma sai Fauzan ya bayar da sanarwar rufe tashar a jiya ba tare da bayyana wani dalili na yin hakan ba.
Da dama daga cikin ma’aikatan wurin dai suna danganta hakan ne da rashin samun kudade daga gwamnatin Saudiya wadda take daukar nauyin wadannan tashoshi, sakamakon sabuwar siyasar yariman kasar, wanda yake kokarin nisanta kasar daga duk wani abu da ya shafi addini, har ma da akidar ta wahabiyanci, inda ya rungumi dabi’u irin na yammacin turai.