Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau da jijjifin safiya ne gungun yahaudawan sahyuniya suka kaddamar da wani farmaki a kan makabartar annabi Yusuf da ke garin Nablus a gabar yamma da kogin Jordan.
Wannan farmaki dai ya zo ne a daidai lokacin da yahudawan suke shirin shiga wurin, amma matasan Falastinawa suka hana su, amma daga bisani tare da taimakon jami’an tsaron yahudawa, sun afka a cikin wannan wuri mai alfarma.
A kowace shekara yahudawa sukan yi irin wannan ta’annuti a kan wannan wuri mai albarka, inda kabarin annibi Yusuf (AS) yake.
Ko a shekarar da ta gabata ma sun kai irin wannan farmaki kuma suka ci zarafin Falastinawa da suke garin na Balatah a cikin gudumar Nablus, inda suka jikkata mutane da dama.