IQNA

23:53 - July 07, 2018
Lambar Labari: 3482813
Bangaren kasa da kasa, majalisar dokokin kasar Thailand ta kada kuri'ar amincewa da daftarin dokar hukunta jagororin addinin buda masu barnata dukiyar kasa.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a zaman da majaisar dokokin kasar ta Thailand ta gudanar a jiya, ta kada kuri'ar amincewa da daftarin dokar hukunta jagororin addinin buda masu barnata dukiyar al'umma.

Jagororin addinin buda a kasar Thailand dai suna da matsayi na musamman, inda wasu daga cikinsu suke yin amfani da wannan damar cin karensu babu babbaka kan dukiyar kasar da sunan addini.

Dukkanin 'yan majalisar dokokin kasar su 117 ne suka amince da wannan daftarin doka, wanda zai bayar da damar hukunta jagororin addinin na buda kasar, wadanda ake kallon sun fi karfin doka.

3728231

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: