IQNA

23:55 - August 01, 2018
Lambar Labari: 3482850
Bangaren kasa da kasa, an kara adadin musulmin da suke zuwa hajji daga kasar Kenya wanda yanzu ya kai mutane 4631 a shekarar bana.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Yusuf Anzibu shugaban kwamitin aikin hajji na kasar Kenya ya seda cewa, an kara adadin musulmin da suke zuwa hajji daga kasar wanda yanzu ya kai mutane 4631 da za su sauke farali a wannan shekara.

Ya ci gaba da cewa wannan babban ci gaba ne aka samu, domin zai kara taimakawa wajen rage yawan musulmin da suke son sauke faralai, amma ba za su iya zuwa ba saboda adadin ya cika.

A shekarar da ta gabata mutane 3800 ne suka sauke farali daga kasar ta Kenya.

Shugaban hukumar ahazan ta kasar Kenya yace sun cimma wannan matsaya ce tare da mahukuntan kasar Saudiyya a wannan shekara.

3735076

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: