IQNA

23:49 - August 03, 2018
Lambar Labari: 3482859
Bangaren kasa da kasa, ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Aljeriya ta bayar da umarnin dakatar da yin amfani da wani kwafin kur'ani mai tsarki a kasar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Aljeriya ta bayar da umarnin dakatar da yin amfani da wani kwafin kur'ani mai tsarki da ake kira Alhaziq a kasar sakamakon wasu kurakurai da aka samu a cikin bugun nasa.

Ma'aikatar ta ce baya ga dakatar da sayar da shi da kuma yada a cikin kasar, an kuma bayar da umarnin hana buga shi a dukkanin fadin kasar.

Ma'aikatar kula da addini a Aljeriya da farko bata gano kurakuran da ke cikin bugun wannan kwafin kur'ani ba, sai bayan buga shi tare da raba shia makarantu da masallatai, inda malamai suka gano hakan.

3735454

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Aljeriya ، umarnin ، addini ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: