IQNA

An Gano Gungun Wasu Masu Safarar 'Yan Ta'adda Zuwa Turai Daga Tunisia

23:50 - August 04, 2018
Lambar Labari: 3482862
Bangaren kasa da kasa, Jami'an tsaron kasar Tunisia sun gano gungun wasu mutane masu safarar 'yan ta'adda daga kasar zuwa nahiyar turai.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Tashar talabijin ta Sky News ta bayar da rahoton cewa, jami'an tsaron na Tunisia sun gano hakan ne ta hanyar samun wasu bayanai na asiri, wadanda suka tabbatar da cewa ana yin amfani da fasfo na bogi domin safarar wasu mutane daga kasar zuwa wasu kasashen turai.

Bayan gudanar da binciken kwakwab kan lamarin, an iya gano cewa mutanen da suke yin wannan aiki sun hada da 'yan kasar Iraki da kuma wasu 'yan kasar ta Tunisia ne, wadanda suke da alaka da 'yan takfiriyya masu da'awar jihadi.

Dukkanin 'yan ta'addan da aka fitar da su zuwa kasashen turai ta hanyar Tunisia suna dauke da fasfo na bogi na kasashen Iraki ko kuma Turkiya.

3735474

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، takfiriyya ، Tunisia ، turai
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :