IQNA

23:43 - August 05, 2018
Lambar Labari: 3482864

Shirin Bayar Da Horon Hadar Kur’ani Mai Taken Imamain

Bangaren kasa da kasa, an fara aiwatar da wani shiri na koyar da hardar kur’ani mai taken Imamain a garin Samirra na Iraki.

Shirin Bayar Da Horon Hadar Kur’ani Mai Taken Imamain

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Qaf cewa, a jiya ne aka fara aiwatar da wani shiri na koyar da hardar kur’ani mai taken Imamain a garin Samirra na Iraki a hubbaren da ke birnin.

Wannan shiri dai zai dauki tsawon watanni biyu ana aiwatar da shi, inda dalibai dari ne da suka cika sharudda aka dauka a matsayin zangon farko na shirin.

Ana koyar da hardar kur’ani mai tsarki a kowace rana na wasu shafukan kur’ani, inda akan yin takara a da yamma da dare kuma akan koyar da wasu ilmomi na addini.

Baya ga hakan kuma akwai wasu shirye-shiryen da ak gudanarwa a kowace rana wadanda za su taimaka ma daliban da suke cikin shirin ta fuskar koyon harada da kuma sauran ilmomi na kur’ani.

3735891

 

 

 

 

 

captcha