IQNA

23:52 - August 07, 2018
Lambar Labari: 3482871
Bangaren kasa da kasa, wata cibiyar musulmi a gabashin Saudiyya ta sanar da shirinta na taimaka ma maniyyata da wani tsari na sahihin karatun gajerun surorin kur’ani.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na albayan ya bayar da rahoton cewa, wata cibiyar musulmi mabiya mazhabar Ahlul bait a gabashin Saudiyya ta sanar da shirinta na taimaka ma maniyyata da wani tsari na sahihin karatun gajerun surorin kur’ani ta hanyar wayar salula.

Cibiyar ta bayyana cewa za ta yi hakan ne omin amfanin alhazai da suke da karancin sani kan kur’ani da kuma karatunsa da suka zo daga kasashen duniya musamman ma kasashen yamamcin turai da gabashin Asiya ko latin.

Za a tsara shirin ne a cikin application na musamman, wanda za a saka gaerun surorin kur’ani da kuma koyar da sahihin karatunsu, gami da saka wasu fitattun makaranta kur’ani na duniya, da yadda suke karanta wadannan surori.

3736662

 

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: