IQNA

An Tarjama Littafin Rayuwan Jagoran Juyin Juya Hali

23:45 - August 09, 2018
Lambar Labari: 3482876
Bangaren kasa da kasa, an tarjama littafin rayuwar jagoran juyin juya halin muslunci na Iran a kasar Iraki.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an tarjama littafin rayuwar jagoran juyin juya halin muslunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei a kasar Iraki, wanda yake Magana a kan rayuwarsa tun daga kuruciya har zuwa zama jagora.

Wannan littafi dai an tarjama shi daga harshen farisanci zuwa harshen larabaci, wannan littafi ya tabo wasu muhimman lamurra da suka shafi rayuwarsa yadda yake gudanar da ita cikin sauki, ba tare da yin fariya ba.

Daga ciki kuwa har da yadda yake rayuwa a cikin gida irin wanda mutane masu matsakacin hali suke rayuwa a cikin irinsa, kamar yadda bisa dabi'arsa baya saka tufafi masu tsada, haka nan kuma yakan ci abinci irin wanda sauran mutane suke ci.

Baya ga haka kuma an tabo rayuwarsa tare da marigayi Imam Khomeni (QS) wanda shi ne bababn malaminsa wanda kuma kasance tare da shi tsawon shekaru har zuwa samun nasarar juyin juya hali.

3737193

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha