IQNA

23:45 - August 10, 2018
Lambar Labari: 3482880
Bangaren siyasa, Ayatollah Imam Kashani limamin da ya jagoranci sallar juma'a a nan birnin Tehran ya bayyana cewa jamhoriyar musulinci na cikin yaki da rudun tattalin arziki na makiya kuma cikin yardar Allah za ta fita daga wannan matsala.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Ayatollah Muhamad Imami Kashani limamin da ya jagoranci sallar juma'ar birnin Tehran ya yi ishara kan tayin Shugaba Trump na Amurka na tattauna da Shugaba Rouhani, inda ya ce manufar makiya shi ne karin matsin lamba ga Iran domin su cimma manufofinsu, wanda kuma hakan bai zai sanya jamhoriyar musulinci ta Iran din ba ta meka wuya.

Yayin da yake ishara kan nuna karfi na Amurka, makirci da makarkashiya na haramtacciyar kasar Isra'ila, da kuma kokarin amfani da kudi wajen sayan Duniya daga mahukuntan Ali-sa'oud, Ayatollah Muhamad Imami Kashani ya ce wajibi al'ummar Iran su kasance masu basira kan irin makarkashiriya da ake kulawa kasar, sannan kuma su kare hadin kansu domin ci gaban kasar, sannan ya bukaci dukkani masu rike da madafun iko na kasar suke ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin basira.

A wani bangare na khodubartasa, Ayatollah Muhamad Imami Kashani ya bukaci bangaren shari'a da su dauka tsautsaran matakai kan wadanda suke yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa da kuma maso boye kaya.

3737307

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: