IQNA

23:55 - August 13, 2018
Lambar Labari: 3482888
Bangaren kasa da kasa, sakamakon killacewar da Isra’ila take yi wa yankin zirin Gaza ana fama da matsalar karancin magungunan ciwon daji.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ana fama da matsalar karancin magungunan ciwon daji sakamakon killacewar da Isra’ila take yi wa yankin zirin Gaza.

Sharaf Qudrah kakakin ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ya bayyana cewa, sakamakon matsalar da ake fuskanta ta fuskar killawacewar da Isra’ila takewa yankin Zirin Gaza, masu fama da cututtuka na musamman suna cikin mawuyacin hali.

Ya ce babbar matsalar da aka fi fama da ita ce karancin magungunan ciwon cutar daji, domin su ne suka fi wahala, kuma da dama daga cikin masu fama da wannan matsala na bukatar fita waje, amma babu halin hakan.

3737868

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، gaza ، karancin ، magunguna
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: