IQNA

23:59 - August 13, 2018
Lambar Labari: 3482890
Kakakin ma'aikatar tsaro a hukumar tseratar da kasa ta Yemen ya bayyana cewa, dukkanin makaman da Saudiyya ta yi amfani da su wajen kai hari kan motar bas ta yara 'yan makaranta, makaman Amurka ne.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, 

Tashar talabijin ta Almasirah ta kasar Yemen ta bayar da rahoton cewa, a yau an gudanar da janazar kananan yara da jiragen yakin saudiyya suka yi wa kisan gilla a ranar Alhamis da ta gabata a yankin Dahyan da ke cikin gundumar Sa'adaha  kasar Yemen.

Mutane fiye da hamsin suka rasa rayukansu, da suka hada da kananan yara talatin, ayyin da wasu da dama suka samu raunuka.

A nata bangaren ma'aikatar tsaron kasar ta Yemen ta nuna tarkacen makaman da Saudiyya ta yi amfani da su wajen kai harin, wadanda dukkaninsu makamai ne na kasar Amurka, wadanda kasar ta Saudiyya take saye daga kamfanonin makamai na gwamnatin Amurka.

3738149

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، yemen
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: