IQNA

23:52 - August 14, 2018
Lambar Labari: 3482892
Bangaren kasa da kasa, Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya taya al'ummar Lebanon murnar cikar shekaru 12 da nasarar da suka samu a kan Isra'ila a yakin kwanki 33 da ta kaddamar a kan kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin wasu wasiku biyu da ya aike wa takwaransa na Lebanon Jubran Basil, da kuma babban sakataren kungiyar Hizbullah sayyid Hassan Nasrullah, Zarif ya bayyana ranar yau 14 ga watan Agusta da cewa rana ce mai tarihi ga al'ummar Lebanon da dukkanin masu 'yanci a duniya, tare da yin fatan alhairi ga al'ummar kasar da kuma masu fafutuka domin tabbatar da adalci.

A ranar 14 ga watan Agustan 2006 ne aka kawo karshen yakin kwanaki 33 da Isra'ila ta kaddamar kan kasar Lebanon, inda ta sha kashi a hannun dakarun Hizbullah, wanda hakan ya tilasta Isra'ila neman majalisar dinkin duniya da wasu manyan kasashe su shiga tsakani domin dakatar da yakin, sakamakon ruwan makamai masu linzami da ta sha daga mayakan Hizbullah na Lebanon.

3738572

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: