IQNA

23:52 - August 22, 2018
Lambar Labari: 3482913
Bangaren siyasa, Shugaban kasar Iran ya aike da sakon taya murnar babbar sallah ta lahiya ga shugabannin kasashen musulmi tare da musu fatan alheri.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna, a sakon taya murnar ranar babbar sallah ta lahiya da ya aike ga takwarorinsa na kasashen musulmi a jiya Talata: Shugaban kasar Iran Dr Hasan Ruhani ya fayyace cewar dukkanin al'ummar musulmin duniya zasu iya kai wa ga matsayin samun kusanci ga Allah matukar suka zage dantse.

Kamar yadda ta hanyar yantar da kai da mika kai ga Allah, zasu iya kai wa ga matakin kawo karshen tarin matsalolin da suke addabarsu musamman matsalar ta'addanci da kashe-kashen rayuka da suka zame ruwan dare gama duniya a wannan rayuwa tamu ta yau.

Dr Ruhani ya kara da cewa: Al'ummar musulmi zasu iya kyautata rayuwarsu ta nan gaba da zata kasance cikin zaman lafiya da sulhu gami da wanzar da adalci da kaunar juna a tsakaninsu.

A jiya Talata ce aka gudanar da bukukuwan sallah a wasu kasashen musulmi, yayin da sauran kasashen suke gudanar da nasu bukukuwan sallar a yau Laraba ciki har da Jamhuriyar Musulunci ta Iran sakamakon sabanin ganin watan Zul-Hajji.

3740646

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: