Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Adel Rasmi wani kirista ne mai sana'ar sayar da nama wanda ya kasance tsawon shekaro yana taimaka ma musulmia duk lokacin idin babbar salla a lardin Mina.
Adel yana samar da raguna a duk lokacin idin babbar salla, baya ga haka kuma yana sayar da su ga musulmia cikin farashi mai rahusa domin masu karamin karfi su samu damar yin layya.
Haka nan kuma yana taimaka wa wajen ayyukan gyaran naman da musulmi suka yanka a matsayin gudunmawarsa a gare su.
Wannan kiriosta ya zama abin buga misali ga al'ummar yankin saboda kyawawan halayensa da kuma kyautatawarsa ga musulmi.