IQNA

23:54 - August 28, 2018
Lambar Labari: 3482932
Bangaren kasa da kasa, hubbaren Imam Hussain (AS) ya girmama wasu mata da suka nuna kwazo kan lamarin kur’ani.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne bangaren kula da harkokin kur’ani na hubbaren Imam Hussain (AS) ya girmama wasu mata da suka nuna kwazo kan lamarin kur’ani a karkashin cibiyar.

Wannan mataki ya zo da nufin kara karfafa gwwar mata wajen bayar da himma a kan lamarin kur’ani mai tsarki.

A kowace shekara ana gudanar da taruka na gasa da kuma na karatun kur’ani a karkashin wannan cibiya, kamar yadda kuma akwa wasu tsare-tsaren na bayar da horon hardar kur’ani.

3742095

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: