IQNA

23:54 - August 29, 2018
Lambar Labari: 3482935
Bangaen kasa da kasa, Muhammad Mukhtar Juma’a ministan ma’aikatar da harkokin addini a Masar ya bayyana cewa ana wani shiri na daukar nauyin mahardata kur’ani.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Muhammad Mukhtar Juma’a ministan ma’aikatar da harkokin addini ta Masar a cikin wani bayaninsa a jiya, ya tabbatar da cewa ana yunkurin fara aiwatar da wani shiri na daukar nauyin mahardata kur’ani mai tsarki a kasar.

Ya ce wannan shirin zai kasance tsakanin ma’aikatarsa da kuma ma’aikatar kula da walwalar jama’a ta kasar ne, inda za su dauki nauyin wasu daga cikin mahardata kan lamurran rayuwarsu.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, bisa la’akari da cewa, bisa la’akari da cewa adadin yana da yawa, za a fara daukar utane 95 daga wadanda suka kaddamar ad sunayensu su 1957.

Daga ciki akwai mata da maza, wadanda za su tallafi da zai taimaka musu a rayuwarsu da kuma daukar nauyin wasu bukatunsu, domin su mayar da hankali ga lamarinsu hardarsu ta kur’ani.

 

3742623

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: