IQNA

A Yau Ne Ake Gudanar Zaben 'Yan Majalisar Dokoki A Kasar Mauritania

0:01 - September 02, 2018
Lambar Labari: 3482943
Tun da safiyar yau ne al'ummar kasar Mauritania suka fara kada kuri'unsu domin zabar 'yan majalisar dokokin kasar da kuma na kananan hukumomi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tun da misalin karfe 7 na safiyar yau ne al'ummar kasar Mauritania suka fara kada kuri'unsu domin zabar 'yan majalisar dokokin kasar da kuma shugabannin kananan hukumomi na kasar.

Tun a shekara ta 2013 ce dai aka gudanar da zabe makamancin wannan, duk kuwa da cewa jam'iyyun adawa na kasar sun kaurace wa zaben a wancan lokacin, amma  a wannan karon jam'iyyun adawa sun shiga zaben, wanda hakan ne ya kara wa zaben na wannan karon armashi matuka.

Tun a farkon wannan makon ne masu sanya ido kan zaben suka fara isa kasar, daga bangaren majalisar dinkin duniya da kuma kungiyar tarayyar turai gami da kungiyar tarayyar Afrika.

A tsakiyar shekara ta 2019 mai kamawa ce dai ake sa ran za a gudanar da zaben shugaban kasa a kasar ta Mauritaniya.

3742981

 

 
captcha