IQNA

Pentagon Ta Dakatar Da Tallafin Dala Miliyan 300 Da Take Bawa Pakistan

23:54 - September 03, 2018
Lambar Labari: 3482950
Bangaren kasa da kasa, Ma'aikatar Tsaron Amurka Pentagon ta bada sanarwan dakatar da tallafin dalar Amurka miliyon 300 da take bawa kasar Pakistan.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, Ma'aikatar Tsaron Amurka Pentagon ta bada sanarwan dakatar da tallafin dalar Amurka miliyon 300 da take bawa kasar Pakistan sanadiyar abinda ta kira rashin bada hadin kai na gwamnatin kasar ta Pakistan dangane da lamuran tsaro a yankin.

wata majiya ta shaida mata cewa shugaban Donal Trump ya ce a jinkirta bada kudaden tallafin a farkon wannan shekara kafin ya yanke hukuncin dakatar da tallafin kwatw-kwata a jiya Asabar. 

Tun lokacinda shugaban Trump ya shiga fadar white house kasashen biyu suke samun sabani a tsakaninsu. Gwamnatin Amurka ta na zargin Pakistan da goyon bayan yan ta'adda a suke cikin kasar Afganistan wanda ya jawo yaduwar ayyuykan ta'addaci a duk fadin kasar. Amma gwamnatin kasar Pakistan ta musanta wannan zargin.

3743399

 

 

captcha