IQNA

23:51 - September 06, 2018
Lambar Labari: 3482959
Bangaren kasa da kasa, wata tawagar manyan jagororin mabiya addinin kirista a Masar sun bayar da kyautar kur'ani ga gwamnan lardin Minya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga jaridar Alwatan News cewa, a jiya ne wata tawagar manyan jagororin mabiya addinin kirista a Masar sun bayar da kyautar kur'ani ga gwamnan lardin Minya na kasar ta Masar Qasem Hussain Qasem.

Bayanin ya ci gaba da cewa, wadannan kiristoci sun kai ziyara a babban ginin jahar inda a nan ofishin gwamnan na Minya yake, inda suka gana da shi.

Ganawar tasu ta mayar da hankali kan muhimamnci ci gaba da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin dukkanin al'ummar kasar Masar kamar yadda aka sansua  tarihinsu.

Hak nan kuma bayan kammala ganawar tawagar kiristocin ta mika kyautar kwafin kur'ani mai tsarki ga gwamnan na Minya.

3744511

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: