IQNA

23:47 - September 07, 2018
Lambar Labari: 3482960
Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya gana da shugabannin kasashen Rasha da kuma Turkiya a yau.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habrta cewa,

Jagoran ya fara ganawa ne da shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyib Erdogan kafin fara zaman shugabannin kasashen Iran, Rasha da kuma Turkiya a yau a birnin Tehran,

A yayin ganawar jagora ya jaddada muhimmancin hada karfi da karfe tsakanin kasashen musulmi, domin warware matsalolinsu da kansu ba tare da wasu bangarori sun yi musu katsalandan ba.

Haka nan kuma jagora ya yi ishara da irin yanayin da aka haifar na hada musulmi fada da juna a daidai lokacin da Isra'ila take cin karenta babu babbaka a kan al'aummar musulmi na Palastine, yayin da musulmi kua sun shagala da junansu.

Shi ma a nasa bangaren shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyib Erdogan ya bayyana rashin hadin kai tsakanin musulmi da cewa, shi ne babban abin da ya jawo kasashen turai suke yin abin da suka gada ma a kan kasashen musulmi, kuma matukar musulmi ba su farka ba, to kuwa za su ci gaba da ganin cin fuska da kaskanci.

Daga bisani kuma a yammacin yau jagora ya gana da shugaba Putin na Rasha, inda suka tattauna  akan muhimman batutuwa da suka shafi alakar Iran da Rasha, da kuma sauran batutuwa na siyasar kasa da kasa, musamman halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya.

3744716

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: