IQNA

23:30 - September 21, 2018
Lambar Labari: 3483001
Bangaren kasa da kasa, rahotanni daga Palastine na cewa a yammacin yau sojojin yahudawan Isra'ila sun harbe wani matashi bafalastine a gangamin da ake gudanarwa a cikin Gaza, domin nemen hakkin Falastinawa da Isra'ila ta kora domin su dawo kasarsu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kakakin ma'akatar kiwon lafiya a Gaza ya sanar da cewa, akalla mutum daya ya yi shahada a yammacin yau, bayan da sojojin Isra'ila suka harbe shi da harsashin bindiga a wannan gangami da ake yi duk a ranar Juma'a.

Wani likita a asibitin garin Gaza Ashraf Qudwa ya bayyana cewa, sojojin na Isra'ila sun harbi matashin mai shekaru ashirin da biyar,  kuma a nan take ya yi shahada, yayin da kuma wasu mutane dari uku da sha biyu suka samu raunuku, hamsin da hudu daga cikinsu an harbe su ne da harsasai masu rai, hudu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.

Dubban Falastinawa ne suka shiga jerin gwanon na yau, domin kara jaddada matsayinsu na kin amincewa da mamaye yankunansu da yahudawa ke ci gaba da yi, tare da neman a maido da 'yan uwansu da aka kora daga kasarsu aka mayar da su 'yan gudun hijira a kasashe makwabta.

3748656

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، harbe ، bafalastine ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: