IQNA

An Bude Ofishin Karbar Ta’aziyyar Shahidan Ahwaz A Najeriya

23:47 - September 29, 2018
Lambar Labari: 3483019
Bangaren kasa da kasa, an bude ofishin karbar ta’aziyyar shahidan Ahwaz a birnin Abuja na Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ofishin jakadancin Iran a Najeria ya bude ofishin karbar ta’aziyyar shahidan Ahwaz a birnin Abuja.

Tun bayan kai harin ta’addanci a garin Awaz wanda ya yi sanadiyyar utuwar mutane fiye da ashirin, ofishin jakadancin na Iran a Najriya yake ta karbar sakonnin ta’aziyya daga jama’a daban-daban, da suka hada da jami’an gwamnatin da ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa da sauransu.

Daga bisani an bude ofishi na musamman domin karbar sakonnin na ta’aziyya, inda jami’an diflomasiyya na kasashe daban-daban suke ta mika sakonninsu.

Daga cikin jakadun da sukea  wurin har da na wasu kasashen Asia da suka hada da China, India, Pakistan da Philipines da sauransu.

Najeriya ma na daga cikin kasashen da suke fuskatar barazanar ‘yan ta’adda masu dauke da akidar kafirta kafirta musulmi, wadanda suka addabi kasar da kuma kasashe makwabta.

3751218

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha