IQNA

An Fara Gasar Kur’ani Karo Na 40 A Kasar Saudiyya

23:57 - October 04, 2018
Lambar Labari: 3483027
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai sarki ta duniya a karo na arbain a kasar saudiyya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an fara gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai sarki ta duniya a karo na arbain a kasar saudiyya da ake a kowace shekara.

Wannan gasa dai kimanin makaranta da mahardata 115 ne daga kasashen duniya 82 suke samun halartar ta, kuma an agudanar da ita ne a bangarori hudu, da suka hada da harda, kira’a da tajwidi da kuma tafsiri.

An gudanar da taron share fage a jiya, inda wadanda suka samu suka tsallake za su kai ga sauran matakai nag aba, kuma za a kammala gasar ne bayan kwanaki hudu a masallacin manzon Allah da ke Madina munawwara.

Sheikh Abdallah bin Ahmad Alfaqih, Walid Bin Huzam Alatibi, Abdullah bin Ata’allah alhussaini su ne manyan alakalan mataki na farko na gasar.

3752711

 

 

 

 

 

captcha