IQNA

23:48 - October 09, 2018
Lambar Labari: 3483035
Bangaren kasa da kasa, jagororin majami’un kiristoci a kasar Ghana sun yi kira da a rika kiyaye kyawawan dabiu.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin wannan makon ne jagororin majami’un kiristoci a kasar Ghana suka yi kira da a rika kiyaye kyawawan dabiu a cikin zamantakewar al’umma.

Babbar manufar wannan kira dai ita ce tabbatar da cewa, an samu wanzuwar amincia  cikin al’umma, tare da nisantar duk wani abu wanda zai iya kawo rashin jituwa tsakanin mutane.

Daga cikin wadanad suka yi wannan kira har da babban mabiya darikar Katolika na kasar Ghana, wanda ya kirayi ma’aikatan gwamnatin kasar da su rike gaskiya a cikin ayyukansu.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, yin ayyuka na gari suna babban tasiri a cikin al’umma, kamar taimakon marassa karfi, da samar da ababe ga mabukata da dai sauransu ayyuka makamantan hakan.

Ghana na daga cikin kasashen Afrika ta yamma da musulmi da kiristoci suke rayuwa tare ba tare da aji tsakaninsu ba.

3754282

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: