IQNA

23:16 - October 17, 2018
Lambar Labari: 3483049
Bangaren kasa da kasa, Alkaluman da Ma'aikatan Cikin gidan Birtaniya ta fitar ya nuna cewa masu gyamar addinin musulmi a kasar na karuwa.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna, Ma'aikatar cikin gidan kasar Birtaniya ta fitar da wani rahoton kan batun gyarar addini a wannan talata, inda ta ce cikin shekarar da ta gabata farmakin da aka kaiwa musulmi a kasar ya karu daga kashi 9 zuwa 40.

Alkaluman da ma'aikatar cikin gidan ta fitar ya tabbatar da cewa a shekarar da ta gabata masu gyamar addini musulimci sun kai farmaki so dubu 49 da 98 a kasar, idan kuma aka kwatamta da shekaru biyar da suka gabatar, harin ya rubunwa so biyu.

Rahoton ya ce fitar Birtaniya daga kungiyar tarayyar Turai da kuma harin ta'addancin da aka kai kasar a shekarar 2017 na daga cikin ilolin da suka janyo kara gyamar musulmi a kasar ta Birtaniya.

Daga cikin nau'in farmakin, harda gona masallatai, cin zafafin Mata masu sanye da hijabi, da kuma izgili da wanda yake sanya da tufafin musulmi a kasar ta Birtaniya.

 

3756656

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: