IQNA

23:15 - October 27, 2018
Lambar Labari: 3483076
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaro a lardin Dayyali na Iraki sun bankado wani shirin ‘yan ta’adda na kai hari kan masu ziyara arbaeen.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Bagdad yaum ya habarta cewa, jami’an tsaro a lardin Dayyali na Iraki sun samu nasarar bankado wani shirin ‘yan ta’adda na kai hari kan masu ziyara arbaeen da suke bi ta cikin lardin.

Bayanin ya ce jami’an tsaro dakuma sojin sa kai fiye da dubu 20 ne suke gudanar da ayyukan tsaro a cikin lardin Dayyali domin tabbatar da cewa an bayar da kariyar da ta dace ga masu ziyarar arbaeen da suke ratsawa ta cikin wannan lardi.

Yanzu haka dai ‘yan ta’addan da aka kame an samu muggan makamai da bama-bamai tare da su, wadanda suke da nufin yin amfani da su wajen kai hari a kan masu ziyara.

3758972

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، bama-bamai ، arbaeen ، iraki
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: