IQNA

23:53 - November 05, 2018
Lambar Labari: 3483103
Bangaren kasa da kasa, musulmin kasar Canada sun nuna alhini kan harin da aka kaiwa wata majami’ar yahudawa a Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, muuslmi mazauna birnin Toronto kasar Canada sun nuna alhini kan harin da aka kaiwa wata majami’ar yahudawa a Amurka a lokacin da suke ibada.

Wannan mataki ya zo ne a matsayin nuna goyon bayan ga mabiya addinai da kuma nuna adawa da duk wani aikin ta’addanci a kan kowane bangaren mabiya addinai ne aka kai shi.

A cikin makon da ya gabata ne wasu mahara suka kai hari kan mabiya addinain yahudanci a wata majami’a a kasar Amurlka, inda suka kasha mutane bakawai daga cikinsu tare da jikkata wasu, muuslmin Amurka sun nuna alhini kan lamarin, musamman ma ganin cewa akwai yahudawa da dama wadanda basu nuna kiyayya ga musulmi a Amurka da ma wasu kasashen turai..

Yahudawa da dama a kasar ta Vanada sun nuna jin dadinsu dangane da wannan mataki da muuslmi suka dauka, inda suke kallon hakan amatsayin lamari mai kyau da zai kara hada kan mabiya addinai.

3761285

حلقه‌ صلح مسلمانان کانادا به یاد قربانیان کنیسه آمریکا/ انگلیسی
 
حلقه‌ صلح مسلمانان کانادا به یاد قربانیان کنیسه آمریکا+ عکس
 
حلقه‌ صلح مسلمانان کانادا به یاد قربانیان کنیسه آمریکا/ انگلیسی

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: