IQNA

Kuwait Da Tunisia Sun Rattaba Hannu Kan Wata Yarjejeniya Ta Kur’ani

23:56 - November 12, 2018
Lambar Labari: 3483120
Bangaren kasa da kasa, kasashen Kuwait da Tunisia sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya wadda ta shafi kur’ani mai tsarki tsarki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Arab Alyaum cewa, Fahad Affasi minister mai kula davharkokin addini na Kuwait, da kuma Ahmad Azum ministan ma’aikatar kula da harkokin addini Tunisia sun rattaba hannu kan yarjejeniyar da ta shafi ayyukan kur’ani.

Bayanin ya ce an rattaba hannu kan wannan yarjjeniya nea  kasar Tunisia a ziyarar da ministan na Kuwait ya kai kasar, inda suka cimma matsaya kan yin aiki tare a bangarori daban-daban da suka shafi kur’ani mai tsarki.

Haka nan kuma yarjejeniyar ta shafi shirya gasar kur’ani waddaza ta hada bangarorin biyu, inda za su gudanar da ayyuka na hadin gwiwa a wannan fage a cikin kasashensu.

Babbar manufar hakan dai ita ce kara yada lamarin kur’ani a cikin al’ummomin kasashen biyu, musamman ma matasa masu tasowa a wanann lokaci, wadanda suke bukatar tarbiya irin ta kur’ani mai tsarki.

3763037

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha