IQNA

23:48 - November 13, 2018
Lambar Labari: 3483121
Bangaren kasa da kasa, Bahram Qasemi ya bayyana harin Da Isra’ila ta kai kan ginin tashar al-aqsa da cewa aiki ne na ta’addanci.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Bahram Qasemi ya bayyana harin Isra’ila kan ginin tashar talabijin ta al-aqsa da ke Gaza da cewa aiki ne da ya cancanci Allawadai.

Y ace ko shakka babu Isra’ila bata taba boye manufarta wajen yaki da duk wani alami na addini ko zamantakewa ko wani abu mai alaka da rayuwar al’umma da jin dadinsu ba, inda takan kai hare-haren dabbanci a kan komai.

Qasemi ya kirayi sauran kasashen duniya da su sauke nauyin da ke kansu na takawa Isra’ila burki kan kisan kiyashin da take yi wa al’ummar Palastine tsawon fiye da shekaru 70 da suka gabata har zuwa yau.

3763646

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، takawa ، isra’ila
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: