IQNA

22:46 - November 16, 2018
Lambar Labari: 3483130
Bangaren kasa da kasa, an fuskanci matasala a ranar farko da aka sanya domin komawar tawaga ta farko ta ‘yan kabilar Rohingya zuwa kasar Myanmar daga Bangaladesh.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Arakan ya bayar da rahoton cewa, a jiya an fuskanci matasalar komawar tawaga ta farko ta ‘yan kabilar Rohingya zuwa kasar Myanmar daga Bangaladesh kamar yadda aka tsara, saboda rashin zuwan wadanda suka kudiri aniyar komawa don kashin kansu.

An tsara a ranar jiya dukkanin ‘yan kabilar Rohingya da suke gudun hijira a kasar Bangaladesh da suke da nufin komawa Myanmar don kashin kansu da su hallara a bakin iyakokin kasashen biyu, babu wani daga cikinsu da ya hallara.

Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira  akasar Bangaladeh Muhammad Abu kalam ya bayyana cewa, sun halarci yankin Kokas dake kan iyaka da Myanmar tun a safiyar jiya, amma babu wani daga cikin ‘yan gudun hijirar Rohingya da ya zo wurin.

Ya ce sun tanadi daruruwan motocin bas-bas domin jigilar ‘yan gudun hijirar zuwa Myanmar, bayan cimma matsaya kan hakan tare da hukumomin Myanmar, amma a halin yanzu wannan magana ta rushe.

 

3764378

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: